Alhaji Umaru Useni Gabari shugaban AMATA na kasa ya ce bisa kiyasi gurguncewar kasuwanci sanadiyar kalubalen tsaro a yankin arewacin Najeriya musamman a jihohin Borno da Yobe a shekaru ukun da suka shude an yi asarar fiye da nera tiriliyan goma sha daya. Ya ce idan an duba yadda mutanen kasashen dake makwaftaka da Najeriya dake shigowa ta jihohin zuwa yin kasuwanci kafin barkewar rigingimu ba karamin kudi Najeriya ta yi asara ba. Tsakanin masu sayar da kaya da kamfanonin dake sarafasu da mutanen dake ketare iyakokinmu su shigo da kudadensu domin yin kasuwanci ba karamin asara kowa ya yi ba. Da ana zuwa Kano a sayi kaya wasu kuma a Maiduguri zasu tsaya su sayi kayansu amma duk wannan babu su yanzu sanadiyar rashin tsaro.
To sai dai Alhaji Gabari ya ce akwai alamun alamura zasu daidaita a wannan shekarar ta 2014 musamman ganin yadda ake kara zaman lafiya a yankin. Ya ce Allah ya fara kawo ahuwa kuma fata suke a samu zaman lafiya mai dorewa a wannan shekarar.
A kasuwance a Kano shugaban ya ce sun fara ganin alamura sun soma daidaituwa. Misali shekarar 2013 ta fi zaman lafiya da ta 2012.
A cigaban neman zaman lafiya a yankin na arewa maso gabas ya sa al'ummar garin Potiskum ta bakin Alhaji Gambo Barau Potiskum suka yi kira ga gwamnan Yobe Ibrahim Geidam ya roki bankuna su bude ofisoshinsu domin a cigaba da hada-hadar kasuwanci kamar yadda aka saba. Ya ce idan an yi biyan albashi banki daya tilo dake bude a garin sai mutum ya je ya tararda mutane fiye da dari biyar kan layi. Wasu sai sun je Azare ko Damaturu ko Misau ko Gombe su dauko kudi. Yan kasuwa sun shiga cikin kuncin halin rayuwa.Ya roki gwamnan jihar ya shiga maganar ya sa bankunan su dawo da ayyukansu a garin Potiskum domin suna ganin zaman lafiya ya dawo.
Ga karin bayani.