Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 36 Sun Mutu A Uganda Sakamakon Ambaliyar Ruwa


Mutanen Uganda a cikin ruwan ambaliya
Mutanen Uganda a cikin ruwan ambaliya

Hukumomi a kasar Uganda sun ce adadin wadanda suka mutu daga ambaliyar ruwar da kuma zaizayar kasar da aka shafe mako daya ya karu zuwa mutane 36 kana kuma ya bar dubbai a makale bayan da wamakon ruwan ya mamaye yankin da tsaunuka suke.

Wamakon ruwan saman da aka shafe mako guda ana yi ya haddasa ambaliyar ruwa da kuma zaizayar kasa a yankunan Bugisu da Bundibugyo da ke kusa da dutsen Rwenzori na gabashin Uganda.

Mai magana da yawun kungiyar bada agaji ta Red Cross a Uganda, Irene Nakasita, ta ce aikin bincike da kuma ceto a yankin da abin ya fi Kamari yawancin ruwa ya mamaye hanyoyi.

Ta ce sun yanke shawarar samar da wani wuri na wucin gadi har sai al’amura sun koma daidai. Don haka ta yiwu cibiyar wucin gadi ta Bubukwang za ta samar da gidaje na kusa mutane 700 wadanda suka rasa muhallansu daga yankin Bundibugyo.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG