A Najeriya, manazarta da yan siyasa na ci gaba da tsokaci akan hukuncin da kotun tarrayya ta yanke, na daure tsohon Gwamnan Jihar Abia kuma babban mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa Sanata Orji Uzor Kalu.
Wani lauya mai zaman kan sa a Abuja Isa Bello ya ce “ba lallai ne Orji Kalu ya shafe wadanan shekarun a gidan kaso ba, domin kuwa yana da damar daukaka kara zuwa kotun gaba. Don haka ana hasashen zai daukaka kara, haka kuma ana iya daukan lokaci mai tsawo ana shari'ar tunda za a koma ne a sake sauraron karar ba ki daya”.
Shi ma wani jigon dan siyasa a Jihar Zamfara Dr. Sani Abdullahi Shinkafi, ya ce wanan alamu ne na “sakamakon aikin da tsohon Gwamnan Jihar Abia yayi”.
Ya kara da cewa “kuma mun ji dadi da hukuncin da kotu ta yanke. Kamata yayi ma duk wani tsohon gwamna kada a biya shi kudin fansho domin suna cutar talakawa, bayan sace kudin jama’a, sai kuma su zo duk wata ana biyan su miliyoyin kudi da sunan fansho. Ai wannan zalunci ne”.
Amma a ra’ayin mai sharhi Abubakar Aliyu Umar, “wanan dai kukan kurciya ne, haka kuma hukuncin zai zama izna ga masu rike da mukaman siyasa, su gane cewa ba wanda ya fi karfin doka”.
Sanata Orji Uzor Kalu shi ne babban mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa kuma tsohon gwamna na uku da kotu take yankewa irin wannan hukuncin a Najeriya.
An kwashe shekaru 12 ana kai gwaro da mari a shari'ar da hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzki zagon kasa ta shigar inda aka tuhumi Orji Uzor Kalu da laifuka 39, da suka hada da hada baki tsakanin sa da kamfanin sa ‘Slok Nigeria Limited’ da wani Darakatan kula da kudaden fadar gwamnatin Jihar Abia har na Naira Biliyan 7.6.
Cikakken sautin rahoton:
Facebook Forum