Mun bude makarantar koyar da harkar fina-finai bisa tsari irin na kasar Amurka inda ake koyar da dalibai harkar fim a hannu guda, kuma don a samu biyansu kudi kamar yadda ake yi a kasashen waje.
Ya ba da misali cewa bayan an koyar da dalibi zama darakta, makarantar idan ta samu aiki ta hada darakta na ainihi da dalibi ya koyi karatu, za su biya shi kudi na aikin da ya gudanar.
Ya ce makarantar an yi mata rijista karkashin hukumar kula da jami’o'i, sannan suna dauko malamansu ne daga wasu jihohin Najeriya kuma wadanda suka karanci harkar fim ko waka domin samun inganci a harkokin fina-finai.
Ya ce wannan makaranta na samun dalibai maza da mata, kuma daga cikin ka’idojin da ake bukata sai dalibi ya tabbata yana da cancanta ta makin "credit" guda biyar, kafin a ba shi gurbi a makarantar.
Sannan da zarar an kammala diploma ko certificate, dalibi na da damar samun gurbi a jami’a kai tsaye.
Kamar kowacce makaranta, ya ce sukan fuskanci matsalar sai dalibi ya bi dukkanin ka'idoji sai kwatsam, dalibin ya daina zuwa. Sai suka gano cewa iyayensu ne suke hana su, ko sun sami gurbi a wata jami’a.
A saurari cikakken rahoton wakiliyar DandalinVOA Baraka Bashir.
Facebook Forum