Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mummunan Harin Da Aka Kaiwa Ma'aikatan Wanzar Da Zaman Lafiya a Congo


Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya yayi Allah wadai da kakkausan harshe kan harin ranar Alhamis da aka kaiwa ma’aikatan MDD dake aiki kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda akalla ma’aikatan wanzar da zaman lafiya ‘yan kasar Tanzaniya 15 da sojojin Congo 5 suka mutu.

Da yammacin jiya Juma’a ne mambobin kwamitin sulhu na MDD suka gudanar da wani taro a asirce domin tattauna batun harin, bayan da suka yi shiru na wani ‘dan lokaci domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu.

Baya ga mutanen da suka mutu, sama da mutane 50 sun raunata a harin da aka kai Arewacin yankin Kivu, inda kungiyar ‘yan tawayen Uganda da aka fi sani da ADF ke a yankin.

Wani jami’an MDD ya fadawa Muryar Amurka cewa ana zargin cewa kunigar ADF na da hannu a harin na ranar Alhamis.

A wata sanarwa da aka fitar jiya Juma’a, Kwamitin ya bayyana jimaminsa da kuma ta’aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu a harin, da kuma gwamnatin Tanzaniya da Jamhuriyar Dimokardiyyar Congo, sai kuma shirin wanzanr da zaman lafiya a Congon da aka fi sani da MONUSCO.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG