Taron nazari da binciken dabarun tsaro na kwana uku zai fara ne da soma duba nasarori da irin wahalhalun da aka fuskanta a fannin tsaro daga lokacin da aka kafata ta yadda za'a gyara tafiya a yakin da kasar Niger ta kaddamar da yaki akan ta'addanci.
Mataimakin daraktan cibiyar Abdulaziz Garba ya ce sun gane tsaro ba na hukumar soji ba ne kadai, har da ma al'umma domin daga kansu ya kamata ya fara. Injishi, dalili ke nan da suka tara masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro tare da jama'a daga kowane bangaren kasar su taru su yi nazari na kwana uku. Bayan taron sai su tantance abubuwan da aka fada kana su mikawa gwamnati shawarwarinsu.
Shugaban majalisar karkarar Tawa Adamu Illo dake halartar taron na da kwarin gwuiwar tasirin shawarwarin da za'a fito dasu a karshen taron amma ya gargadi kasashe renon Faransa da su sake salon gudanar da tsaro.
Hukuma ko ta sojoji ko ta 'yan sanda basu isa ba tabbatar da tsaro ba, a cewarsa. Hadin kan jama'a na da mahimmanci wajen cimma nasara a yaki da ta'addanci. Adamu Illo ya yi misali da Najeriya inda ya ce akwai tsaro amma ba'a musgunawa jama'a. Idan wani ya shiga matsala da jami'an tsaro shi ya jawo ma kansa. Kamata ya yi a matsayinsu na kasashe masu 'yancin kai su san yadda zasu gudanar da harkokin tsaronsu ta damawa da jama'a.
Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani.
Facebook Forum