Alkalin da ya jagoranci mukabalar da aka yi tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da malaman Kano, Sheikh Salisu Shehu ya ayyana cewa malamin ya kaucewa dukkan tambayoyin da aka masa.
A ranar Asabar aka gudanar da mukabalar a ma’aikatar shari’ar Kano.
Bayan da ya kammala sauraren bangarorin biyu, Sheikh Shehu ya ce Sheikh Kabara ya yi ta zagaye-zagaye wajen amsa tambayoyin da aka masa, lamarin da ya sa ya gaza gamsar da masu sauraren shi.
A watan Fabrairun wannan shekara gwamantin Kano, ta dakatar da malamin daga gudanar da karatu a makarantarsa saboda da zarginsa da yin batanci ga Annabi (S.A.W.,) zargin da Sheikh Kabara ya musanta.
“A daukacin lokacin da ya kwashe yana magana, Mallam Abduljabbar ya kaucewa dukkan tambayoyin da aka masa.” Alkalin mukabalar ya ce, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Akalin ya ce da farko Abduljabbar ya yi korafin cewa babu isasshen lokaci sannan ya kuma nemi da a yi mukabalar maudu’i daya bayan daya.
“Amma kuma shi ne ya rika cakuda maudu’an yana hada su ba tare da ya ba da amsa ba.”
Sai dai a martanin da ya mayar, Sheikh Abduljabbar ya ce ba a sanar da shi ka’idojin mukabalar ba, yana mai jaddada cewa ba a ba si isasshen lokacin da zai gabatar da hujjojinsa ba.
Wannan mukabala na zuwa ne bayan da wasu malamai a jihar Kano, suka ja hankali akan cewar, fatawar Sheikh Kabara na iya haifar da hatsaniya, don haka gwamnati ta ga cewar akwai bukatar daukar matakin rufe makarantarsa.
A baya gwamnatin jihar Kano ta saka ranar 7 ga watan Maris na wannan shekara, a matsayin ranar da za a gudanar da mukabalar a fadar Sarkin Kano, amma daga baya a dage zaman.