ACCRA, GHANA - Makwanni biyu kafin a dawo zaman Majalisar Dokoki, a watan Janairun 2023 babbar jam’iyar adawa ta NDC, ta yi wasu manyan sauye-sauye a shugabancin marasa rinjaye a Majalisar, inda ta nada tsohon mataimakin ministan harkokin kudi, Dakta Cassiel Atto Forson, ya maye gurbin ‘dan majalisa mai wakiltar Tamale ta kudu, Alhaji Haruna Iddrisu, a matsayin shugaban marasa rinjaye, matsayin da ya rike na shekaru shida. Haka kuma aka sauya mataimakin shugaban da kuma mai ladabtarwar jam’iyar a Majalisa.
Wannan ya haifar da cece-kuce, hatta a tsakanin ‘yan jam’iyyar, inda suka yi ikirarin cewa ba a sanar da su ba kafin a yanke shawarar sauya su.
A cikin shekarar 2023, wasu jami’an gwamnati mai ci da shugaban kasa ya nada, sun samu kansu tsundum cikin ce-ce-ku-ce da ya dauki lokaci ana yi a kasar.
Tsohuwar ministar tsabta da albarkatun ruwa, Cecilia Abena Darpah, ta kai karan wasu masu yi mata aikin gida cewa sun yi mata sata, wanda bincike ya kai ga samun makudan kudade a gidanta, da suka hada da dalar Amurka miliyan daya, da Yuro dubu dari uku. Bayan jama’a sun yi ta korafe-karafe, ministar ta yi murabus.
Manyan jam’iyun Ghana biyu, wato jam’iyar NPP mai mulki, da babbar jam’iyar adawa ta NDC sun zabi ‘yan takaran da za su tsaya musu a zaben shugaban kasa mai zuwa, cikin watan Disambar 2024. NPP ta zabi mataimakin shugaban kasa, Dokta Mahamudu Bawumia, sai NDC ta zabi tsohon shugaban kasa, Dakta John Dramani Mahama.
Lauya Anas Mohammed, ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa an gudanar da zabe lafiya, ta hanyar bin doka daga ‘yan siyasa da masu kada kuri’a.
Tun da tattalin arzikin kasar Ghana ya shiga wani hali na tabarbarewa a 2022, gwamnati Ghana ta fara tattaunawa da asusun lamuni na duniya (IMF) don neman taimako a watan Yulin 2022.
Sai a watan Mayun 2023 ta yi nasarar samun rancen dala biliyan uku, kuma a ranar 17 ga watan Mayun ta samu kashin farko na kudin, dala miliyan dari shida, kuma har ya zuwa yanzu kasar na bin dokokin da asusun lamunin ta gindaya, don farfado da darajar cedi da wasu bangarorin tattalin arziki.
Kamar yadda editan jaridar Daily Guide, Alhaji Abdul-Rahman Gomda ya nuna, tallafin na tasiri kuma yana da burin a wannan shekarar gwamnati ta ci gaba da gyara darajar cedi.
Kamar yadda muka fara gani, kudin Cedi ya fara tasowa, kuma kudin man fetur da disel bas u karu ba, ba kamar yadda muka saba gani. Don haka, muna fata shekarar 2024 gwamnati za ta tabbatar da alkawarin a ta dauka; Cedi ya tsaya inda yake, kudin man fetur kuma ya tsaya inda yake. Ko da bas u sauko ba, to kada su haura.
A bangaren ilimi kuma, a farkon shekarar 2023, jami’oin Ghana suka fito da sabbin karin kudaden da dalibai za su biya, fiye da kashi 15 cikin 100 da gwamnati ta kara. Bayan kuka da al’ummar kasa suka yi, ministan ilimi, dakta Yaw Osei Adutwum ya sa baki, aka janye wannan karin.
Haka kuma ‘yan kwangilan dafa abinci kyauta ga ‘yan makaranta suka shiga yajin aiki, wanda ya dauki lokaci sannan aka samu dacewa tsakaninsu da gwamnati kan kudadensu da ba a biya su ba.
A hulda tsakanin kasa da kasa, Ghana ta amshi bakwancin mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Haris a watan Maris din 2023. A watan Mayu, Firai Ministan Japan, Fumio Kishida ya kai ziyara Ghana daga cikin rangadinsa na Afrika. Haka kuma Ghana ta amshi baki daga kasashen afrika daban daban, a tarurrukan kasa da kasa da dama da aka gudanara a kasar.
Malam Seeba Shakibu, babban sakataren jam’iyar PNC reshen Accra, ya bayyanawa Muryar Amurka inda yake son gwamnati ta baiwa tasiri a shekarar nan ta 2024. Yace:
Yana son gwamnati ta yaki cin hanci da rashawa, kuma ta hana sarrafa dukiyar gwamnati inda bai dace ba domin kara kimar kudin Cedi na Ghana, da kuma kara darajar tattalin arzikin kasa gaba daya.
Kasar Ghana ta shiga alhinin mutuwar wasu fitattun mutane a shekarar da ta gabata. Daga cikinsu akwai, uwargidan tsohon shugaban kasa, John Kufour, wato Theresa Kufour, da tsohon ministan wasanni, E.T Mensah; da dan kwallon kafa da ya mutu a girgizar kasa da ya auku a Turkiya, Christian Atsu; da fitacciyar marubuciya, Ama Ata Aidoo; da fitaccen lauya, Akoto Ampau da sauransu.
Saurari cikakken bitar daga Idris Abdullah:
Dandalin Mu Tattauna