Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mu Muka Kashe Albani Zariya - in ji Shekau


Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria
Sheikh Muhammad Awwal Albani Zaria

Kungiyar Jama’atu lil da’awati wal jihad, da aka fi sani da Boko Haram, ta dauki alhakin kashe shahararren malamin addinin Musulunci daga garin Zariya mai suna Sheikh Muhammad Awwal Albani da kuma barazanar kashe wasu sarakuna da malamai.

A wani sauti, an ji wani mai murya irinta mutumin dake ikirarin shine shugaban kungiyar Abubakar Shekau yana cewa “Albani Zariya, mu muka kashe shi. Albani Zariya, mu muka kashe shi. Shekau ya kashe Albani Zariya.”

Sai dai kuma, kungiyar bata yi bayani akan hare-hare akan garuruwan Konduga da Izghe ba, wanda jami’an tsaron Najeriya ke dorawa alhakin hakan akan kungiyar.

Wannan shine sako na farko da kungiyar ta fitar na farko, tun bayan hare-hare akan jihohi Borno da Adamawa da ya kashe mutane sama da dari biyar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:12 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG