Binciken da aka sake gudanarwa a Birtaniya ya tabbatar da wanda aka yi tun farko inda masu bincike basu sami kwararrun shaidun da suka tabbatar da amfanin motsa jiki ga masu fama da ciwon bacin rai ba.
Masu binciken sun dauki tsawon lokaci suna kyakkyawan sa ido a kan gwaje gwaje talatin da biyar da aka yi a kan mutane dubu daya da dari uku da hamsin da shida wadanda suka tabbatar suna fama da ciwon tsananin bacin rai. Masu fama da cutar da suka rika motsa jiki bisa ga shawarwarin da wani asibitin motsa jiki ya basu suna nuna alamun samun sauki sosai.
Bayan gwada wadanda suka motsa jiki, da wadanda suke shan magani kadai, masu binciken sun gano cewa, wadanda suka motsa jiki sun fi wadanda suka sha magani samun sauki.
Masu binciken sun gano cewa, motsa jiki yana da amfani kamar taimakon mai ciwon da shawarwari. Sai dai suka ce, sakamakon binciken ya nuna yanayin mutanen da aka gudanar da binciken a kansu ne kawai ba za a iya sanin ko haka zata faru ga dukan jama’a ba.
Duk da wannan ci gaban da aka samu a fannin binciken, masanan sun ce ana bukatar kara yin bincike da kuma gwaje gwaje kafin a san ko motsa jiki zai taimaka wajen jinyar ciwon.