Gwamnati ta bayyana cewa, za a gudanar da shirin ne domin inganta hanyoyoyin yaki da cutar a cikin gida a maimakon ci gaba ga dogara ga kasashen waje, wannan kuma zai zama da taimako a kokarin yaki da cutar kafin shekara ta dubu biyu da gomas ha biyar.
MInistan lafiya na Najeriya ne ya bayyana haka a wajen wani taro kan yaki da cutar kanjamau da aka yi a jihar Lagos. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya zata ci gaba da bada karfi wajen yaki da cutar kanjamau. Yace shugaban Najeriya ya bayyana shirin da yake da shi na yaki da cutar kanjamau tare da kara yawan kudin da ake kashewa kowacce shekara da dala miliyan dari.
Ministan ya bayyana cewa, gwamnatin tana kokari sosai a yaki da zazzabin cizon sauro, yace an raba sama da gidan sauro miliyan sittin tsakanin shekara ta dubu biyu da goma zuwa yanzu. Banda haka kuma yace ana kyautata zaton cewa, a watan Disamba zata a tabbatar da cewa yanzu Najeriya ta shawo kan kurkunu. Dr. Chuku yace yanzu an yi shekara hudu ba a sami wani dauke da cutar kurkunu ba.