Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kogi: 'Yansanda Dubu 12 Aka Jibge Domin Zaben Gwamnan Jihar


Babban Sifeton 'Yansandan Najeriya Mr. Solomon Arase
Babban Sifeton 'Yansandan Najeriya Mr. Solomon Arase

Domin a tabbatar an gudanar da zaben gwamnan Kogi ba tare da tashin hankali ba ko matsala mahukuntan Najeriya sun jibge 'yansanda dubu goma sha biyu a jihar.

Gobe Asabar ne za'a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi lamarin da ya sa aka dauki tsauraran matakan tsaro tare da kara 'yansanda dubu 12.

Kazalika rundunar 'yansandan Najeriya tace ta shirya tsaf ta tabbatar da tsaro lokacin zaben. Mataimakin sifeto janar na 'yansandan kasar mai kula da sashen ayyuka a hedkwatarsu dake Abuja DIG Watonye Wakama shi ne zai sa ido a zaben.

Ya yiwa wadanda ke shirin yin kafar angulu ga zaben kashedi tare da cewa sun kewaye jihar da 'yansanda masu dimbin yawa domin tabbatar da komi ya tafi daidai. Ya kuma gargadi jama'a da su shiga hankalinsu saboda doka zata yi aiki kan duk wanda ya saba mata..

Hukumar zaben ta samarda ma'aikata 13,100 da zasu gudanar da aikin zaben. Kwamishanan zaben na jihar Kogi Husseini Halilu Pai yace kawo yanzu sun raba kayan aiki a duk kananan hukumomi 23 dake jihar. Sun kuma yi shirin ko ta kwana dangane da naurar tantance masu kada kuri'a. Sun samarda kwararru akan naurar da zasu dinga zagayawa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG