Sama da mutane miliyan guda masu amfani da wayar Android ne aka yaudara suka sauke manhajjar WhatsApp ta bogi.
Ita dai wannna manhaja ta bogi an kirkireta ne ta yadda mutane ba zasu iya gane banbanci tsakanin ta gaskiyar da ta bogi ba. Da zarar mutum ya sauke manhajar a waya zai fuskanci matsala, domin manhajar da kanta zata fara sauke wasu manhajojin, ta kuma bude hanyar da tallace-tallace za su yi yawa a waya.
Abin dubawa shine ya aka yi har sama da mutane miliyan guda suka sauke wannan manhaja ta jabu. Masana harkokin fasaha na ganin wadanda suka kirkiri manhajar jabun sun tsara ta kamar yadda ya kamata domin tabbatar da ganin babu wanda ya ankara.
Cikin makon nan kafar WhatsApp ta sabunta siffofinta inda ta kara wata fasaha da in mutum ya aika da sako cikin minti bakwai zai iya goge sakon a wayar wanda ya aikawa.
A kwanan nan ne kamfanin Facebook ya bayyana cewa a rahotansa na rabin shekara, mutane dake amfani da kafar WhatsApp sun karu sun kai Biliyan guda.
Facebook Forum