Kasancewar rahin aikin yi ga matasa na kawo tashin hankali tsakanin al’umma, hakan yasa gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da wannan shiri na noman Alakama na rani, wanda gwamnatin zata taimaka musu da kayan aiki.
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya gayawa mahalarta taron bitar da za a yi domin wayar da kan manoma akan noman rani na alkaman cewa, tun da dai Kaduna bata daga cikin jerin jihohin dake da albarkatun man Fetur, ya zama wajibi a rungumi noma kasancewar sai da noma ake rayuwa.
Game da tsarin da gwamnatin Kaduna zata bi wajen samo matasa kusan 5000 wajen noman rani, tare da basu kayan aikin da suka hada da Taki da Iri da kuma maganin kashe Kwari. Haka kuma bayan sun noma akwai wanda zai sayi kayan kudi hannu.
Mallam El-Rufa’i, yace jihar Kaduna itace ta daya wajen Noman Masara da Waken Soya da Citta dakuma Tamatiri da Rake, hakan yasa gwamnatin ta ware kananan hukumomi Biyar da aka tabbatar za a iya noman Alkama, domin a baiwa matasa damar samun aikin yi.
Wasu daga cikin matasan dake cikin shirin sunyi godiya da gwamnatin jihar Kaduna. Ana sa ran matasan da suka fito daga kananan hukumomi Hudu na jihar Kaduna, zasu kwashe kwanaki Uku suna koyan harkar noman rani na Alkama.
Domin karin bayani ga rahotan Isah Lawal Ikra.