Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Faransa Ya Fara Ziyara a Jamhuriyar Nijar


Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron

Shugaban Faransa ya fara ziyara a kasar Nijar yau, ziyarar da wasu ke ganin tamkar ta kwantar da hankulan 'yan Nijar ne saboda shugaban Faransan ya tsallake kasarsu a ziyararsa ta fako zuwa nahiyar Afirka watan jiya.

Yau Juma'a 22 ta watan Disambar 2017 shugaban Faransa, Emmanuel Macron, zai isa jamhuriyar Nijar inda zai fara ziyararsa ta farko zuwa kasar tun lokacin da ya kama ragamar mulkin kasarsa wadda ta yiwa Nijar din mulkin mallaka.

A yayin ziyarar da zai kammala gobe Asabar, Emmanuel Macron zai ziyarci sansanin sojojin kasarsa dake girke a Yamai da sunan yaki da ta'addanci. Zai kuma shiga shagulgulan bukukuwan Kirsimati da ake yi a kasar.

Ana kyautata zaton shugaban zai tattauna da takwaransa na Nijar kuma mai masaukinsa Shugaba Mahamadou Issoufou akan batun da suka shafi dadaddiyar hulda dake tsakanin kasashensu.

Jakadan kasar Faransa dake Nijar shi ya je shaidawa shugaban Nijar cewa Emmanuel Macron zai fara ziyara a kasar yau kamar alkawarin da ya yi tun farko a taron da suka yi a Paris makon jiya akan tsaron kasashen yankin Sahel. Zai jaddada goyon bayan Faransa na ganin masu hannu da sshuni sun cika alkawarin ba da taimako wajen yakar ta'addanci a yankin Sahel, musamman a Nijar.

Nijar dai an yi mata alkawarin dalar Amurka biliyan 23 a wajen taron na makon jiya.

A watan Agustan 1960 ne Jamhuriyar Nijar ta samu 'yancin mulkin kai daga Faransan amma har gobe ita ce take da iko akan karfen uranium da ake hakowa da Nijar din ke tinkaho dashi.

To saidai masu fashin baki na ganin ziyarar ta Emmanuel Macron a matsayin matakin kishin laifi ne bisa la'akari da yadda jama'a suka fusata saboda zarginsa da ketare Nijar lokacin da ya ziyarci kasashen Ivory Coast, Burkina Faso da Ghana watan jiya.

Souley Mummuni Barma na da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG