Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Lallasa Mali A Wasan Afirka U-23


Junior Ajayi ne ya jefa kwallaye biyu, sai kuma Muhammed Usman ya jefa ta ukun a a yayin da Najeriya ta lallasa Mali da ci Uku da biyu a wasan share fage na ‘yan kasa da shekaru 23 na Afirka da aka buga a Senegal.

‘Yan wasan Mali ne suka fara nuna alamun samun nasara a wasan, amma suka kasa ci gaba da rike ragamar wasan wanda hakan yaba dan wasan Najeriyar Ajayi damar jefa kwallo a raga a cikin minti gama sha shidda da fara wasan.

Yayin da Usman ya kara wa ‘yan wasan Najeriyar azama da jefa kwallo ta biyu a cikin minti na 34, wanda ya sa jikin ‘yan wasan na mali yayi sanyi tamkar wasan ya zo karshe.

Bayan hutun rabin lokaci ‘yan sawan na Mali suka zage damtse yayin da suka jefa kwallaye biyu. Adama Niane ne ya jefa kwallo ta fari a minti na 55 da fara wasan, sa’an nan Suleyman Sissoko ya jefa ta biyu bayan minti goma.

Yanzu haka dai Najeriya na kan gaba a cikin rukunin B da maki uku, yayin da Misira da Algeria suka yi kunnen doki da ci 1 – 1.

Yan wasan Najeriyar za su kara da Misira idan Allah ya kaimu ranar laraba mai zuwa, kuma idan suka sami nasarar lashe wasan, hakan zai basu damar kai wa zagaye kusa da na karshe.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG