Dalibai a Amurka na cigaba da dagewa suna kuma bayyana ra’ayoyin su akan tsarin jam’iyyu biyu kacal da suka kanainaye siyasar kasra, da batun bashin dalibai, da dokoki akan ganyen wiwi, da baki, da kuma mallakar bindiga.
A jihar Kansas dalibai guda shida na kara nuna dagewar su, zasu tsaya takarar kujerar gwamna Kuma ba da wasa suke ba.
Dokar jihar Kansas bata kayyade shekarun wanda zai tsaya takarar kujerar gwamna ba. Daga shekarar da ta gabata zuwa yanzu matasa 6 ‘yan jihar Kansas suka ayyana tsayawa takara. Kuma wadannan matasan sun san abinda suke yi, sun sami kwarin guywa, kuma a shirye suke don neman canji.
Amma matasan masu neman takara, wadanda suke kusan kashi daya cikin uku na sauran ‘yan takara da za su tsaya a zaben fidda gwani a shekarar nan, na gwagwarmaya da shugabancin jam’iyyu don gabatar da koken su (matasan).
Facebook Forum