Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Menene Dalilin Rufe Gwamnatin Amurka?


Wasu da suke zanga zangar kin jinin rufe gwamnati
Wasu da suke zanga zangar kin jinin rufe gwamnati

Tun ranar dagya ga watannan aka rufe gwamnatin Amurka sai yau da aka dawo. To ko menene dalili?

Yau kwana goma sha shida ke nan da aka rufe gwamnatin Amurka wanda ya sa ayyukan gwamnati suka tsaya cik a birnin Washington D C kuma ya koma fanko da rashin motoci da yawa da mutane.

Domin sanin musabbabin dalilin rufe gwamnatin abokiyar aiki Grace Alheri Abdu ta zanta da Alhaji Ibrahim Ahmed da Alhaji Aliyu Mustapha dukansu jigajigan 'yan jarida kuma shugabannin Muryar Amurka. A nashi bayanin Alhaji Ibrahim ya ce abun da ya jawo rufe gwamnati shi ne kasawar majalisa ta cimma daidaito kan kasafin kudi.Abun da ya sa hakan kuwa shi ne hakikijewar da wasu 'yan jam'iyyar Republican suka yi kan cewa sai an cire kudin da aka sa kan fadada shirin kiwon lafiya da zai taimaki marasa galihu wanda aka fi sani da suna Obamacare. Ya ce hakan ya faru tsakanin shekarar 1995 da 1996 lokacin mulkin Bill Clinton shi ma a kan shirin kiwon lafiya da 'yan Republican suka ce dole sai an cire daga kasafin kudi.

Alhaji Aliyu ya yi bayani kan yadda rufewar ta shafi ma'aikatan gwamnati domin da farko an ce wadanda aka ce su koma gida har sai an bude gwamnati ba za'a biyasu ba amma daga baya 'yan majalisa sun yadda a biyasu. Ya ce na farko dai mutane basa son zaman kashe wando a gida. Mutun ya yi kwana 16 ba yin fari bare baki abu ne da bashi da dadi. Na biyu shi ne yanzu ne za'a zo a soma turanci ko za'a biya ko ba za'a biya ba. Na uku mutane sun ga raguwar ababen hawa, wato babu cinkoso a birnin Washington kamar yadda aka saba gani kafin rufe gwamnati. Amma yau da mutane wajen 800,000 sun dawo aiki haka ma cinkoson jama'a da ababen hawa. Yayin da aka rufe gwamnati babu saye da sayarwa kamaar yadda aka saba. Mutane sun takaita kashe kudi domin babau albashi.

A cikin jam'iyyun biyu rufe gwamnatin zai fi shafar 'yan Republican. Alhaji Ibrahim ya ce wasu 'yan tsiraru ne 'yan bangaren tea party dake cikin 'yan Republican suka gabatar da bukatar a cire kudin sabon shirin kiwon lafiya to amma babu daya cikin bukatunsu da suka samu. Ra'ayoyin Amurkawa ya nuna cewa kusan kashi 70 cikin dari suka dorawa 'yan Republican alhakin rufe gwamnatin. An kuma yi kiyasin cewa cikin kwanaki 16 da aka rufe gwamnatin Amurka ta yi asarar dala miliyan dubu ashirin da biyar ($25b).

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:10 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG