Majalisar ta kada kuri’a da tsakiyar dare ta amincewa da gyare gyare a kasafin kudi da za a iya ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati har zuwa ranar 15 ga watan Disamba, yayinda suka bada umurnin a jinkirta aiwatar da Dokar Fadada Ayyukan Kiwon Lafiya ga marasa galihu a kuma janye biyan haraji kan wadansu kayan aikin jinya.
Ganin ana fuskantar yiwuwar dakatar da ayyukan gwamnati da tsakiyar daren Litinin, fadar shugaban kasa ta White House da kuma ‘yan jam’iyar Democrat a majalisar dattijai sun kushewa tsarin na jam’iyar Republican da kakkausar murya, wanda ba zai sami goyon bayan majalisar dattijai ko shugaban kasa ba.
Majalisar wakilai ta kuma amince da ci gaba da biyan sojoji albashi ko da aka dakatar da ayyukan gwamnati.
Tun farko majalisar wakilai da jam’iyar Republican ke rinjaye ta ki amincewa da kudurin majalisar dattijai na ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati zuwa ranar 15 ga watan Nuwamba, yayinda ‘yan majalisar suka ki amincewa da duk wani tsarin da zai bada damar aiwatar da dokar fadada ayyukan kiwon lafiyar.
Dukan majalisun ba zasu zauna ba yau Lahadi. Majalisar dattijai zata zauna gobe Litinin da rana.
Idan majalisun biyu basu cimma matsaya a kan kasafin kudin ba cikin sauri, za a dakatar da dubban ma’aikatar gwamnatin tarayya a kuma daina gudanar da ayyukan gwamnati da dama.