‘Yan Republican masu shugabancin majalisar wakilai sun fasa yin muhawara da kada kuri’a kan wani kudirin da aka yiwa kwaskwarima, bayan da suka farga cewa ba zai sami cikakken goyon baya a majalisar ba, kuma ba zai samu shiga ba a majalisar dattijai.
Shugabannin majalisaar dattijai daga jam’iyar Republican da Democrat da su ka yi zaman dakon yadda abubuwa za su kasance a majalisar wakilai, sun ci gaba da tattaunawa kan kudirin da suka fara musanyar ra’ayi akai.
Kudirorin da duka majalisun dokokin biyu suka gabatar sun amince da sake bude ma’aikatun gwamnati, da kara yawan bashin da kasa za ta iya ci zuwa wani dan gajeren lokaci. Sai dai kudirin majalisar wakilai zai kwaskwarima ga dokar kula da kiwon lafiya da gwamnatin shugaba Obama ta zartas.
Amma wakilai daga jam’iyyar Democrat sun ki goyon bayan hada batun kiwon lafiya ko sauran wasu batutuwa da dokar kasafin kudi.
A cikin wata hira da yayi da tashar talabijin ta New York shugaban Amurka Barack Obama yayi kira ga wakilai su jingine siyasa su daina sanya Amurkawa cikin wahala.
Yadda ‘yan majalisar dokokin Amurka su ka kasa cimma jituwa kan kowane kudiri, ya sa kasar ta kara matsawa daf da ranar cikar wa’adin matakin kara yawan bashi don gwamnati ta iya ci gaba da karbar bashin biyan bukatun ta.