Manyan sarakunan gargajiyan jihar Ekiti, sun bi sawun sauran jama’ar Nigeria wajen kiran da a gudanar da zaben gwamnan jihar da za’a yi Asasbar cikin lumana. Sun roki mutane da su gujewa tashin hankali.
Shugaban majalisar sarakunan jihar Ekiti, Oye na Ekiti Oba Demola Jude, yana cikin sarakunan da suka kira a yi zaben lafiya.
Sarkin y ace ya yi amannar cewa idan ana addu’a komi zai tafi lami lafiya saboda haka ya kira a dukufa ga addu’a, kana su so junansu.
Haka shi ma sarkin Ijero Ekiti, Oba Bayo Adawale, yace mutane su sani cewa ba duka ‘yan takarar gwamnan zasu zama gwamna ba. Mutum daya ne zai ci zabe, saboda haka duk wanda ya lashe zaben a mutunta sakamakon.
Mataimakin babban sifeton ‘yan sandan Nigeria mai kula da ayyukan ‘yan sandan Joshak Habila, ya bada umurnin a janye ‘yan sandan dake tsaron lafiyar manyan mutane. Yace sanadiyar zaben gwamnan da za’a yi a ranar Asabar din nan, duk ‘yan sandan dake kula da lafiyar masu gata su koma hedkwatar ‘yan sandan dake Ado Ekiti da karfe shida na sanyin safiyar Asabar, domin su hada hannu da abokan aikinsu don tabbatar da tsaro a ranar zaben. Ya kara da kwantar da hankalin jama’a yana cewa su kada kuri’unsu cikin kwanciyar hankali.
A saurari rahoton Hassan Umar Tambuwal
Facebook Forum