Malama Fatsuma tace ita kanta tana godewa Allah amma a gaskiya makwabta suna cikin halin- kaka-nika-yi. Tace ma’aikatan gwamnati ko masu sana’ar hanu duk babu abunda yake tafiya.
Da aka gaya mata cewa ai sanannen abu ne ga kowa hali da mutanen Barno da Yobe da sauransu suke ciki, sai ta ce ai na Maiduguri yafi tsanani fiyeda ko wani wuri. Tace sai magidanci ya fita tunda da safe ya taka da kafa zuwa unguwa kamar Bulumkutu ya bar mata da yara, ya dawo hannu banza.
Da aka tambayeta shin ana bude kasuwanni, kuma ina matsalar take ne ana fuskantar karancin kayayyaki ne kodai akwai kaya masu saye ne babu? Sai malama Fatsuma tace ai akwai kayayyaki masu saye ne babu, saboda babu kudi.
Malama Fatsuma tace galibin masu hali sun kwshe iyalansu sun bar Maiduguri. Daga nan tayi kira ga masu hali da hukuma su tallafwa jama’a domin saukaka hali d a suke ciki.
Ga karin bayani.