Maharan sun hallaka jami’an tsaro biyu a wannan harin. A martanin da jami’an suka mayar, sun kashe a kalla goma daga cikin maharan.
Magatakardar ofishin gwamnan jihar Diffa, ya tabbatar ma wakilin Muryar Amurka, Mamane Bako, da faruwar wannan hari. Sai dai duk kokarin jin ta bakin gwamnan bai samu nasara ba.
A jajiberan shiga sabuwar shekara shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou, yayi kira ga ‘yan kungiyar Boko Haram da su ajiye makamansu ganin cewa tura ta kai bango, bayan fatattakarsu da akayi daga dajin Sambisa a Najeriya.
Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan ziyarar da Ministan cikin gida Bazoum Mohamed, ya kai yankin Diffa inda ya karbi mayakan Boko Haram 31 da suka mika wuya. Kuma yayi gargdin cewa korar ‘yan Boko Haram daga dajin Sambisa ka iya watsa su zuwa wasu bangarori na jamhuriyar Nijar.
Domin karin bayani saurari rahotan Mamane Bako.