Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Ya Ja Kunnuwansu Akan Cin Hanci da Rashawa


Babban Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai
Babban Hafsan Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai

An dade ana zargin sojojin Najeriya musamman wadanda suke yankin arewa maso gabas da cin hanci da rashawa tare da yiwa mutane kwace da kuma musguna masu

Babban Hafsan Sojojin kasan Janar Buratai ya ja kunnuwan sojojin Najeriya da su guji cin hanci da rashawa saboda abun da shugaban kasa ya sa a gaba ke nan yana yaka shi ba ba zai barsu ba.

Janar Buratai yace dole ne ya dauki matakan yaki da cin hanci da rashawa musamman a lokacin da sojojin suka soma bude wasu hanyoyi na zirga-zarga. Yace duk wanda aka kama da cn hanci da rashawa zai dandana kudarsa.

Baicin cin hanci da rashawa babban hafsan ya kira sojoji da sauran jami'an tsaro dake yankin su guji tursasawa jama'a ko yi masu kwace. Yace yakamata a yanzu "mu zama 'yanuwan juna mu kuma guji duk abun da zai tursasawa jama'a"

Yace duk sojojin dake yankin ana kula dasu ta yadda ya kamata kuma ana biyansu duk hakkinsu a kan kari saboda haka kada wani ya ba jami'an wasu kudi, inji Janar Buratai.

Ya yabawa jami'an sojojin akan yadda suka nuna kishin kasa wajen yaki da kungiyar Boko Haram. Ya kuma mika godiyarsa ga 'yan jarida da yace sun kasance dasu tun daga farkon rikicin. Ya gode masu da irin rawar da suka taka.

Ya kira sojojinsa da kada su yi sakaci su cigaba da yakin saboda 'yan ta'adan yanzu sun bazu. Basa wuri daya kamar da. Yanzu lokaci ne na sa ido da yin takatsantsan domin a zakulosu a duk inda suke. Yace dole a bi 'yan ta'adan duk idan suke kada a bari su sake taruwa tare.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG