‘Yan sanda a Nepal sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, wani jirgin saman fasinja ya rikito yayin da yake kokarin tashi a babban birnin kasar, Kathmandu, inda aka yi nasarar ceto matukin daga tarkacen jirgin dake ci da wuta, sai dai dukkanin mutane 18 din dake cikin jirgin sun hallaka.
Kakakin rundunar ‘yan sanda kasar Nepal, Dan Bahadur Karki ya bayyana cewar, jirgin mallakin kamfanin jiragen saman na “Sauraya” na dauke ne da ma’aikatansa 2 da kuma ma’aikatan kamfanin 17.
Jami’in hukumar kula da sufurin jiragen saman kasar Nepal, Gyanendra Bhul ya shaidawa AFP cewa, ana gudanar da bincike akan jirgin domin tantance ko matsalar data haddasa hatsarin ta na’ura ce ko kuma ta rashin gyara, sai dai bai yi karin haske akan lamarin ba.
Hotunan bayan hatsarin da rundunar sojin kasar Nepal ta wallafa sun nuna yadda jikin jirgin ya rabe 2 sannan ya kone kurmus.
Sanarwar da rundunar sojin kasar ta wallafa ta bayyana cewar, jirgin ya yi hatsari ne da misalin karfe 5 da rabi na asubahin yau agogon GMT, inda ta kara da cewar martanin gaggawar da tawagarta ta kai wurin ya taimaka wajen aikin ceto.
Kafar yada labarai ta Khabarhub ta ba da rahoton cewar jirgin ya kama wuta ne bayan da ya zame daga kan titin sa.
An tsara cewar jirgin zai yi balaguro ne tsakanin tashoshi mafi hada-hadar a kasar Nepal, Kathmandu zuwa Pokhara, cibiyar yawon bude idanu mai mahimmancin gaske a kasar dake tsaunukan Himalaya.
Dandalin Mu Tattauna