Dakarun Burged ta 6 na rundunar sojin Najeriya dake shiya 3, masu aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Whirl Stroke, sun kama mambobi 4 na kungiyar ‘yan tawayen Ambazonia daga jamhuriyar a Kamaru a jihar Taraba.
An kama mambobin kungiyar da ake zargin ‘yan tawayen Ambazonia ne a wani otel dake karamar hukumar Takum ta jihar.
Sakamakon samun sahihan bayanan sirri a rana r 18 ga watan Disamban da muke ciki, dakarun sun bi diddigi tare da damke mutanen.
A sanarwar daya fitar, mai rikon mukamin mukaddashin darakta kuma kakakin burged ta 6 ta rundunar sojin Najeriya, Olubodunde Oni, yayin binciken farko yace, wadanda ake zargin sun yi ikrarin cewar su wani bangare ne na kungiyar ‘yan tawayen dake da hannu a safarar makamai ta hanyar musayar ‘ya’yan coccoa da abokan hadin bakinsu dake Najeriya.
An kwato wayoyin hannu guda 4 mutanen da ake zargin wadanda suke tsare a yayin da ake cigaba da bincike.
Dandalin Mu Tattauna