A cikin hirarshi da Sashen Hausa, Mallam Shehu Sani ya bayyana cewa, kungiyar zata marawa kungiyar ‘yan keke NAPEP baya da nufin ganin an yiwa wadanda aka kashe adalci ta wajen biyan diyya da kula da iyalansu da kuma hukumta jami’an tsaron da suka dauki wannan matakin.
Tun dama kungiyar tayi barazanar gudanar da zanga zanga a birnin tarayya Abuja ta nuna bacin ranta dangane da kisan da kuma neman gwamnatin tarayya da kuma majalisa su dauki mataki.
Shehu Sani yace kungiyar ta janye shirin zanga zangar ne zuwa mako mai zuwa domin ba hukumomi dama su kafa kwamitin bincike da kuma nazarin matakan ladabtarwa da ya kamata a dauka idan ta kama kamar yadda suka yiwa kungiyar NAPEP alkawari.
Kungiyar NAPEP dai ta bayyana cewa, galibin mutanen da aka kashe a harin da jami’an tsaro suka kai makon jiya a unguwar da aka fi sani da suna “Appo Village” membobinta ne .
Jami’an tsaro sun kai hari kan wani gida da ba a kamala ba, suka kashe mutane kashe mutane tara, da dama kuma suka ji rauni. Mutanen dai bisa ga cewarta wadanda suke zaune a gidan da sanin masu gidan, sai dai jami’an tsaro sun bayyana cewa, sun sami bayanan sirri da suka nuna cewa, akwai ‘yan kungiyar Boko Haram a cikin gidan, bayanin da wadansu daga cikin wadanda aka kama a gidan suka tabbatar.