Shugaba Jonathan ya yi wannan kiran ne bayan ganawarshi da takwaranshi na Amurka Barack Obama yayin taron kolin Majalisar Dinkin Duniya, bayan harin da kungiyar ta’addanci ta al-Shabab ta kai kan wata kasuwar zamani dake Nairobi babban birnin kasar Kenya.
Shugaba Jonathan yace Najeriya tana fuskantar kalubalar tsaro sabili da tashin hankalin da kungiyar Boko Haram mai tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama take yi.
A cikin hirarshi da Muryar Amurka, shugaba Jonathan yace kungiyoyin mayaka basu da hujjar amfani da tashin hankali wajen tirsasawa fararen kaya.
Yace, “yanzu muna fama da wadanda suke kashe mutane kawai ba gaira ba dalili. Sai ka nemi sanin dalili, addini ne? idan addini ne, to karkatacciyar koyarwa ce, domin babu wani addini a duniya da na sani da yace ka kashe mutumin da baka ma sani ba. Na hakikanta cewa, harin ta’addanci a duk inda aka kaishi a duniya, hari ne a kanmu duka, kuma tilas ne kasashen duniya su hada hannu wajen yakui da ta’addanci. Babu wanda yake da wata hujja.”
Shugaba Goodluck Jonathan yace an sami ingancin tsaro ainun tunda aka kafa dokar –ta-baci a wadansu jihohin arewacin Najeriya. Ya kuma jadada cewa, gwamnatinsa zata ci gaba da hada hannu da Washington da kuma sauran kasashen duniya wajen yaki da ta’addanci.
Dangane kuma da batun wutar lantarki shugaba Jonathan yace, an jima ana fama da matsalar wutar lantarki a Najeriya abinda ya gurguntar da masana’antu. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa tana kokari domin shawo kan matsalar. Bisa ga cewarshi gwamnati ta hada hannu da wadansu kamfanoni masu zaman kansu da nufin inganta samar da wutar lantarki.
Shugaba Goodluck Jonathan ya kuma yi tsokaci dangane da rahoton cibiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya “Transparency International” wadda rahotonta na shekara ta dubu biyu da goma sha biyu ya nuna cewa, Najeriya tana matsayi 139 daga cikin kasashe 176 da cibiyar ta bincika a matsayin kasashen da suka fi kowanne albazaranci a duniya.
Shugaba Jonathan yace gwamnatinsa ta dauki matakan shawo kan matsalolin da suka addabi kasar da tafi kowacce yawan al’umma a nahiyar Afrika. Da suka hada da cin hanci da rashawa da albazaranci. Yace kasar zata rika gudanar da ayyyukanta a fili yadda al’umma zata san abinda ke gudana.
Da aka tambaye shi dangane da batun takarar shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, sai shugaba Jonathan yace, “Da farko ina so jama’a su sani cewa, a cikin shekarun da na yiwa kasar nan aiki, ina da kyakkyawar niyya ga ‘yan Najeriya. Ban yi aiki sabili da biyan muradun kaina ba. Ina da kishin kasar nan a zuciyata. Mun fitar da kasar nan daga dogaro ga hanyar samun kudi guda daya inda aka dogara ga man fetir kadai. Yanzu ana maida hankali kan harkokin noma da hakar mu’addinai, da albarkatun mu’addinai, da kuma harkokin sarrafe sarrafe da suka suke taka kyakkyawar rawar gani a fannin tallatalin arzikinmu.”
Shugaba Jonathan ya ci gaba da cewa, “abu guda daya nake so in bari bayan na bar mulki shine cewa, zaben Najeriya ya kasance mai sahihanci da karbuwa. Yadda ‘Yan Najeriya zasu iya zaben wanda suke so ba wanda yake daukar ‘yan banga da makamai suna kwatar mulki ko ta halin kaka ba. Muna kuma kokarin tabbatar da cewa, kuri’ar talakawa tayi tasiri. Ya kamata duniya ta amince da cewa, mun bi tsari da matakan da ya kamata na gudanar da zabe a dukan matakai, kama daga shugaban kasa da gwamnoni da kuma kananan hukumomi.”