Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Layukan Mai Zasu Bace Matukar Dillalai Suka Saya A Wurinmu - Dangote


Aliko Dangote
Aliko Dangote

Dangote, wanda ke jawabi ga manema labaran fadar gwamnatin Najeriya a Abuja, ya bukaci kamfanin man Najeriya (NNPCL) da dillalan man dake fadin kasar su dakata da shigo da man daga ketare.

A yau Talata, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, yayi karin haske akan yadda za’a kawo karshen matsalar dogayen layukan mai a Najeriya wacce ta ki ci taki cinyewa.

Dangote, wanda ke jawabi ga manema labaran fadar gwamnatin Najeriya a Abuja, ya bukaci kamfanin man Najeriya (NNPCL) da dillalan man dake fadin kasar su dakata da shigo da man daga ketare.

Ya kuma bayyana fatan cewar matatar mansa ce za ta warware matsalar layukan ababen hawa a gidajen man dake fadin Najeriya.

“Ina sa ran nnpcl da dillalan mai zasu daina shigo da man daga ketare, kamata yayi su zo su karbi abinda suke bukata. Matukar suka zo suka karba ba za’a sake ganin layukan mai a gidajen man najeriya ba.”

Hakan na zuwa ne kasa da makonni 4 bayan da gwamnatin Najeriyar ta fara aiwatar da manufarta ta sayarwa matatar Dangote da danyen mai da Naira a maimakon dalar Amurka.

Gwamnatin tarayyar tace hakan zai daidaita farashin man a cikin gida tare da karfafa darajar takardar kudin Najeriya Naira ta hanyar rage bukatar dala a hada-hadar danyen man.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG