Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Dangote Ce Ke Samar Da Galibin Man Jirgin Saman Da Ake Bukata A Najeriya - Rahoto


FILE PHOTO: A view shows part of Dangote oil refinery in Ibeju Lekki district
FILE PHOTO: A view shows part of Dangote oil refinery in Ibeju Lekki district

Dillalan man fetur sun bayyana cewar matatar man Dangote ce ke samar da galibin man jirgin saman da ake amfani da shi a Najeriya.

A cewar wani rahoto a kan bayanan makamashi, dillalan man jirgin sama sun bayyana cewar matatar man Dangote, da ka iya tace ganga dubu 650 a rana, ce ke samar da galibin man jirgin saman da ake amfani da shi a cikin Najeriya, kasa da watanni 6 bayan fara aikinta.

“Yanzu muna saye daga matatar dangote, ta dan fi araha ko kuma muce farashinsu daya da wanda ake shigowa dashi daga ketare,” a cewar babban daraktan kamfanin makamashi na Asharami, Foluso Sobanjo, kamar yadda ya fada a tattaunawar da aka yi da shi a rahoton makamashin a wannan makon.

Matatar da ta kasance wani reshe na kamfanin Sahara Group ita ce ke kan gaba wajen samar da man jirgin sama inda ta mamaye kaso 20 cikin 100 na kasuwar.

Sobanjo ya kara da cewa ana sayar da tan daya na man jirgin saman matatar Dangote a kan tsakanin dala 2 zuwa 3 a matsayin rangwame ga masu shigo da shi.

Ya cigaba da cewa motocin masu daukar tan 10, 000 zuwa 20, 000 da ake samarwa koda yaushe daga matatar sun fi dadin saye.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG