A makon jiya ne gwamnatin Lagos ta kama tare da tsare wasu 'yan jihar Jigawa su 121 da suka tafi ci rani Lagos, a dai-dai lokacin da al'ummar Musulmin Jihar Rivers, wadanda galibinsu 'yan arewa ne, suka koka a kan matakin gwamnatin jihar na rusa masallacinsu na Juma'a a birnin Fatakol bisa ikirarin cewa, an gina shi ba bisa ka'ida ba.
Wannan lamari ya kai gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriyan ga shirya taron manema labarai a Kano domin kira ga hukumomin jihohin biyu su daina cin zarafin ‘yan arewa da ke zaune a jihohin nasu.
Shugaban gamayyar kungiyoyin ya bayyana rashin jin dadinsu ga yanda gwamnatin tarayya ta kama baki ta yi shuru a kan wannan batu, alhali ita ce keda hurumin ta shiga ta kwato wa duk dan kasa ‘yancinsa wanda kundin tsarin mulkin Najeriya ya basu cewa zasu iya zama a ko ina a cikin kasar.
Kungiyoyin matasan arewa sun yanke shawarar sa kafar wando daya da gwamnati wurin; an hana baiwa kamfanonin ‘yan kudu kwangila a arewacin kasar. Sun ce za su yi amfani da dokokin kasar wurin tabbatar da ganin an daina baiwa ‘yan kudu ayyukan kamar yanda su kuma suke hana ‘yan arewa a yankunansu.
Tuni dai shi ma tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana damuwa game da matakin, yana mai cewa, zai gabatar da batun a zauren Majalisar Dattawa kasar domin daukar mataki.
To amma a hira da wakilin sashin Hausa a Kano Mahmud Ibrahim Kwari, bayan taro da manema labarai a Kano, wakili a kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin na arewa, Alhaji Ashiru Shariff ya ce kungiyar ba za ta lamunta da matakin gwamntocin jihohin biyu ba.
Ga dai hirar tasu:
Facebook Forum