Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa, Ta Yaya Ake Gane Soyayyar Gaskiya?


Shirin samartaka na wannan makon ya sami zantawa da samari da ‘yan mata daban daban domin jin ra’ayoyin su dangane da yadda ake gane soyayyar gaskiya tsakanin saurayi da budurwa.

Koda shike ba’a taru an zama da yaba, amma masu iya Magana sun ce kowa da irin kiwon da ya amshe shi, dan haka a cewar wata daga cikin wadanda muka ji ra’ayoyin nasu ta ce abu mai sauki ne gano mai son ka da gaskiya bisa la’akari da yadda kuke tafiyar da al’amurran yau da kullum tsakanin ku.

Da shike ra’ayoyin mabam banta ne, wasu daga cikin samarin cewa suka yi babu yadda za’a yi mutum ya gane dari bisa dari da cewa son gaskiya ne saboda a dalilin su, da wuya ka tarar da budurwa da saurayi guda, kuma a kowane lokaci tana iya nuna ma dukan su kauna ala halin wanda take so daban yake.

Daga karshe kuma wasu sun nuna cewar ba a nan take ba, wai an take budari a ka! Babbar matsalar itace abin duniya wato kudi, da zarar kana da kudi to duk yarinyar da ka nema zata nuna maka lallai tana kaunar ka da gaskiya.

Menene ra’ayin ku akan wanna? Ku biyo mu a shafin mu na facebook domin a bayyana ra’ayi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG