Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kunar Gidan Sanata: An Kama Mutane 18


‘Yan sanda a jahar Kano sun kama mutane goma sha takwas da ake zargi da sa hannu wajan kona gidan sanata Kabiru Gaya da wasu matasa suka yi a ranar laraba da ta gabata a karamar hukumar Gaya dake jahar Kano.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jahar Kano DSP Magaji Majiya, kamar yadda ya fadawa kafar sadarwar (NAN) a jahar Kano cewar an sami nasarar kama mutanen ne a yayin da suke aikata laifin.

Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jahar Mr Maigari Dikko ya ziyarci wurin da aka kona kuma ya bada izinin kama wasu mutane biyar wadanda ake zargin su da shirya wannan danyen aiki.

Y ace “mun kama mutane goma sha takwas kuma yanzu haka suna taimaka mana da bayanai a binciken da muke gudanarwa.

“haka kuma kwamishinan ‘yan sanda ya bada izinin kama wasu mutane guda biyar da ake zargi da shirya wannan tashin hankali” a cewar sa.

Daga karshe ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan ya bada izinin tura jami’an tsaro domin inganta tsaro a yankin.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG