Wani alkali a jihar Texas a kasar Amurka, mai shara’a Wayne Salvant, ya jaddada hukuncin daya yakewa wani saurayi Ethan Couch, dan wani attajiri wanda ya kashe mutane hudu da Mota bayan da yayi tatul da giya a shekarar 2013, a lokacin yana da shekaru 16.
Mai shara’a Wayne Salvant, ya yakewa Ethan, hukunci shekaru biyu a gidan yari a matsayi yaro a wancen lokaci a bisa doka yanzu yana da shekaru goma sha tara ya zama cikakken mutu.
Masu gabatar da kara na Gwamnati sun ce wanna shi hukunci mafi tsanani da za’a iya yanke mashi a bisa doka da yadda aka tsaro daga kotun yara inda a nan ne aka fara yanke masa hukunci.
A lokacin da ake yi masa shara’a a shekarar 2013, wani masanin halaiya da tunani dan Adam, wanda ya bada ba’asi akan yaro yace Ethan, ya tashi cikin daula bai san wahala ba saboda haka shi ganin komai yake yi kamar dai dai ne.
A wancen lokaci an same shi da laifin kisa bada nufi ba da kasancewa cikin maye, wanda aka ja masa kunne da kuma sa masa ido har na tsawon shekaru goma, amma daga baya ya sabawa wannan doka da yasa aka koma da shi gaban alkali.