Kungiyar matasa masu ra’ayin gurguzu a Jamhuriyar Nijar, ta bayyana takaicinta game da abin da ta kira "cin fuska da rashin kunyar" da wani dan gwagwarmaya ya yi wa shugaba Issouhou Mahamadou.
Kalaman cin fuskar da kungiyar matasan ke magana akai, ta shafi alfanu ko rashin alfanunn huldar Faransa da kasashen Nahiyar Afirka a wannan lokaci da ake ci gaba da tafka mahawarar watsi da takardar kudi ta CFA.
Yayin wata mahawarar bainar jama’a da ya jagoranta a jiya a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, Shugaban kungiyar Urgences Panafricanistes, Kemi Seba, ya kira shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou a matsayin mai fama da "gushewar hankali."
Seba ya soki bukatar zaman sojan Faransa da shugaba Issouhu ya nuna a yankin Sahel a yakin da ake yi da ‘yan ta’adda.
Jama'a da dama na ganin lafuzzan da shugaban kungiyar masu kyamar kudaden CFA ya yi amfani da su wajen sukar lamirin shugaban kasar Nijar, sun sabawa al’adun al’umomin kasashen Afirka.
Dalilin kenan da ya sa kungiyar matasa masu ra’ayin gurguzu a Nijar kiran taron manema labarai don nuna bacin ranta akan wannan al’amari.
Kungiyar MJS a ta bakin Hajiya Balkissa, na ganin amfani da kalaman batanci wajen bayyana ra’ayi akan koma wacce irin magana ce, abu ne da ya sabawa tsarin fadar albarkacin baki.
Kungiyar Urgences Panafricanistes, wacce ke da rassa a kusan dukkan kasashen Afirka renon Faransa na gwagwarmayarta ne da nufin tayar da matasa daga barci akan maganar yaki da tsarin mulkin mallaka.
Daga cikin irin gwagwarmayar da take yi har da adawa da amfani da kudaden CFA.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum