Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan Nijer Sun Dage Kan 'Yancinsu Bayan Kotu Ta Sako Wasu Shugabanninsu


Shugaba Mahamadou Issoufou.
Shugaba Mahamadou Issoufou.

Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun sako wasu shugabannin matan jam’iyyun hamayya da aka kama a ranar Litinin din da ta gabata lokacin da suka jagoranci wani gangami a kofar jam’iyar RDR Canji ta su tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman.

Madame Bayar Mariama Gamatche da Madame Hadiza Maizama wadanda dukkansu suka taba rike mukamin minista a shekarun baya, da Madame Zeinabou Abani jigo a jam’iyyar RDR Canji, sun fada hannun ‘yan sanda ne a yayin wani gangamin matan jam’iyyun hamayya a ranar Litinin 15 ga watan Maris.

Bayan shafe wuni biyu a hannun ‘yan sandan farin kaya, alkali ya sallami wadannan mata da yammacin jiya Laraba saboda rashin hujjoji akan abin da ake zarginsu da shi. Hajiya Aichatou Ibrahim ita ce shugabar matan RDR Canji ta kasa.

Karin bayani akan: Shugaba Mahamadou Issoufou, Nijer, Nigeria, da Najeriya.

Ta ce “Mu mata ‘ya’yan talakawa da muke shan wahala ne muka shirya taron saboda kwato ‘yancinmu, amma kuma sai aka turo mana ‘yan sanda suka kama iyayen mu.”

A baya hukumomi sun tabbatar da kama daruruwan mutane sanadiyyar zanga zangar watsi da sakamakon zaben da ya gabata cikinsu har da tsohon Firai minista Hama Amadou da Janar Moumouni Boureima mai ritaya da dai wasu jiga jigan jami’iyyun adawa. Wannan na matsayin wani matakin dauki dai dai da hukumomi ke amfani da shi don katse masu hanzari amma kuma kokuwa yanzu aka fara, inji su.

Takun saka ta tsakanin ‘yan adawa da masu mulki bayan fitar da sakamakon zaben aka yi tsakain Bazoum Mohammed da Mahaman Ousman wani abu ne da ke ci gaba da jan hankulan masu rajin kare dimokuradiyya, dalilin kenan da ya sa shugaban gamayyar kungiyoyin ROADDH Son Allah Dambaji ke gargadin wadannan bangarori akan bukatar mutunta doka.

A ranar 23 ga watan Fabrairu ne hukumar zabe ta bayyana dan takarar jam’iyyar PNDS Bazoum Mohammed a matsayin wanda ya lashe zaben 21 ga wata da kashi 55.75 cikin dari. Amma dan takarar RDR Canji Mahaman Ousman ya ce shi ya ci zaben da kashi 50.30 sabili kenan da ya sa ya garzaya kotu, wace ke shirin raba wannan gardama nan da lokaci kadan.

Ga dai rahoton Wakilin Muryar Amurka a Yamai Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG