Wannan batu na zuwa ne yayin da gwamnatin kasar ke maida martani game da bayanan da wani dan jarida da ke da masaniya kan harkokin Boko Haram, Ahmad Salkida ya fitar da ke cewa akasarin ‘yan matan sun mutu.
Yanzu haka dai ‘yan matan makarantar Chibok sun cika shekaru hudu a hannun mayakan Boko Haram, lamarin da ke shan suka daga ciki da ma wajen Najeriya.
Kuma tun a wannan lokaci aka samu kungiyoyi da dama da ke ci gaba da fafutukar ganin an ceto wadannan ‘yan mata.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tun kafin da kuma bayan sace ‘yan matan, ‘yan bindiga masu tada kayar baya na Boko Haram ke ci gaba da sace mutane.
A baya dai gwamnatin kasar ta samu ceto wasu daga cikin ‘yan matan na Chibok ta hanyar shiga tsakani da kuma musayar da aka yi da wasu mayakan kungiyar ta Boko Haram.
Sai dai kuma yayin da gwamnatin kasar ke tutiyar kwato ragowar ‘yan matan na Chibok, yanzu haka wata sabuwa ta kunno inda wani dan jarida da a baya ya taimaka wajen shiga tsakani Ahmad Salkida, ya fitar da bayanai a shafinsa na Twitter da ke cewa cikin yan matan chibok 113 da suka rage a hannun mayakan, yanzu 15 ne ke raye.
Kuma wadanda ma suka ragen an aurar da su ga mayakan Boko Haram kuma har suma sun zama ‘yan kungiyar.
Salkida, wanda ke zauna a Dubai, kuma masani kan harkokin Boko Haram, ya shawarci gwamnatin kasar ne da kafin ta amince da wani yarjejeniya to ta bukaci da a nuna mata ragowar ‘yan matan don sanin ko suna raye ko kuma a’a.
Tuni ma dai iyayen wadannan yan mata suka maida martani da cewa sukan zasu gurfanar da gwamnatin kasar gaban kotun duniya. Mr Ayuba Alamson dake zama kakakin kungiyar iyayen yan matan yace ai kamata yayi gwamnati ta ceto ‘yan matan kamar yadda aka ceto na Dapchi.
Tuni ma dai fadar shugaban kasa ta fitar da martani ta hannun daya daga cikin hadiman shugaban kasar, Malam Garba Shehu, game da bayanan na Salkida inda ta ce bata da wadannan bayanai kasancewar ba ta ji daga wadanda suka sace ‘yan matan ba, ko kuma wadanda ke shiga tsakani na kasa da kasa.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum