A cikin hirar shi da Muryar Amurka, mai taimakawa mataimakin shugaban kasan kan siyasa Abdulrahman Bappah Yola ya bayyana cewa, Osinbajo ya zabi likitocin Najeriya su duba shi don gwada misali da amincewa da kwarewar su.
Abdulrahaman Bappah ya ce kwararrun likitoci shida ne suka yi wa mataimakin shugaban kasar tiyasa a wani asibiti dake Birkin Ikko da aka kamala cikin nasara
Bisa ga cewarshi, Kwararrun likitoci 6 ne na kashi da kashe zafin ciwo su ka yi ma sa aiki a asibitin Duchess da ke Ikeja a Lagos.
A nasa bayanin, Jami'in labarun mataimakin shugaban Laolu Akande ya c ce aikin tiyatar ya yi nasara.
Akande ya ce a na sa ran sallamar Osinbajo a 'yan kwanaki kalilan.
Irin fidda wannan labari na jinyar shugabannin Najeriya a fadar Aso Rock, wani sauyi ne ta fuskar yada labarun da a baya a kan boye da matakan hana yada jita-jita.
Mai taimakawa mataimakin shugaban kasan kan harkokin siyasa Abdulrahman Bappah Yola ya rage kaifin abun da ya faru daga karaya zuwa gurdewa.
Yola ya kara da cewa Osinbajo ya zabi likitocin Najeriya su duba shi don gwada misali da amincewa da kwarewar su.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: