An samu kimanin mata talatin da suka samu kubuta daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram daga dajin Sambisa.
Matan wadanda yanzu haka suke Madagali, ta jihar Adamawa, suce sunyi tafiya ta fiye da kilomita goma kafin su isa garin na Madagali dake makwabtaka da jihar Borno, inda ake tallafa masu.
Da yake tabbatar da labarin shugaban karamar hukumar Madagali, Mr. James Watarda, yace mata talatin da yara ne suka tsira zuwa garin na Madagalin inda karamar hukumar ke tallafa masu.
Yace duk kansu an kaisu asibiti domin a duba lafiyan jikinsu dana ‘yayan su, ya kara da cewa yakamata gwamnatin ta gaggauta taimakamasu.
Matan sun ce sun tsira ne bayan da suka haura Katangar da aka gina a dajin na Sambisa.
A kwanaki ne dai ‘yan Boko Haram suka kai hari a kauyukan kumamza da kuma Munagu-Afayi, inda sukayi awon gaba da mata da kananan yara.
Kawo yanzu hukumomin sojojin Najeriya, bazuyi Karin haske ba dangane da mata da yaran da suka samu suka kubuta.