Jakadan Amurka a Najeriya yace kasarsa da Najeriya sun hada hannu domin aiwatar da ayyuka kamar kafa kamfanin sarafa shinkafa dake Kano. Jakadan yayi jawabin ne yayin da ya kai ziyara a kamfanin dake sarafa shinkafa wanda hukumar raya kasashe ta Amurka ta taimaka aka gina. Jakadan yace ire-iren wadan nan ayyukan yakamata kasashen biyu su dinga yi.
Hukumar raya kasashen ta Amurka tana bada horo akan ayyukan noma. Jakadan yace yayi mamaki akan yawan abincin da ake shigowa dashi daga kasashen waje. Yace Najeriya na iya ciyar da kasashen Afirka ta Yamma gaba daya.
Alhaji Muhammed Mai Fata shugaban kamfanin sarafa shinkafar yace dama can akwai alaka tsakanin kamfanin da hukumar raya kasashe ko USAID a takaice wadda tana karkashin ofishin jakadancin kasar Amurka ne. Hukumar itace take koyar da manomansu tana kuma basu sanshera da sabbin hikimomi na noma da yadda zasu tsaftace anfaninsu kana kamfanin ya sayi shikafar a hannun manoman. Kawo yanzu dai sun yi fiye da shekara uku suna dangantaka tare. Dalili ke nan da jakadan Amurka ya ga ya kamata ya ziyarci kamfanin ya ga me suke yi.
Wasu daga cikin manoman sun fadi albarkacin bakinsu. Wani yace da kafin su samu taimakon horaswa yana samun buhu 55 a hekta guda amma yanzu yana samun buhu 90. Yace an koya masa yadda rai reni iri da yin dashe da yadda zai sa taki. Halima da ta shugabanci kungiyar mata tace sun samu fiye da buhu dari sun sayar har ma sun sayi injin nika shinkafar.
Ban da horas da manoma hukumar USAID zata dauki matakan warware wasu matsalolin da kamfanin ke fuskanta kamar yadda shugaban kamfanin ya bayyana. Babbar matsalar kamfanin ita ce ta wutar lantarki. Gwamnatin Amurka tana shirin ta kawo yadda za'a samu wutar.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.