Jahar Kano, ta shiga cikin jerin jahohi wajen shida da hukumar zaben Najeriya (INEC) ta ayyana zabukansu a matsayin wadanda ba su kammala saboda yawan soke kuri’u. Ga dukkan alamu wadanda su ka zaku su ji sakamakon zaben jahar Kano su na da sauran jira. Da ya ke ayyana zaben na jahar Kano a matsayin mara kammala, Shugaban Hukumar Zabe ta INEC, shiyyar jahar Kano, Furfesa Bello Shehu ya ce ya zuwa lokacin jam’iyyar PDP ta ci kuri’u miliyan daya da dubu 14 da 474 a yayin da ita kuma jam’iyyar APC mai mulkin jahar ta samu dubu dari 987 da 819, a wannan zaben da kuri’u dubu 49 761 su ka lalace.
Furfesa Shehu ya ce an soke jimlar kuri’u dubu 141 da 694 a runfunan zabe wajen 172 a fadin Kano. Ya ce PDP ta zarce APC da kuri’u dubu 26 da 655, to amma dayake kuri’un da aka soke dubu 141 da 691 ne, tanajin hukumar zabe ya hana ayyana irin wannan zaben a matsayin kammalalle. Dalili kuwa shi ne hakan ya hana tabbatar da tazarar da ake bukata tsakanin ‘yan takarar biyu kafin a tabbatar da sakamakon zaben, ma’ana a tabbatar da kammalar zabe. Don haka hukumar zaben ta ayyana zaben na Kano a matsayin mara kammala, kuma za a sanar da ranar da za a sake gudanar da zaben a wuraren da aka soke.
Ga wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:
Facebook Forum