WASHINGTON, DC —
Malama Nafisa Mahmoud Abdullahi matashiya ce wacce ta karanci harkar kasuwanci a Kano state polytechnic ta ke kuma harkar kasuwancin na sayar da kayayyakin kyalkyali na mata dangogin zanin gado, labule da sauransu
Ta ce ta karancin ilimin kasuwanci ne domin ta bunkasa yadda kasuwanci ke tafiya a kasar Hausa, kuma tace karantar kasuwancin da tayi ya taimaka mata wajen yin ma'amala da jama'a.
A yanzu haka a cewarta suna sayen kayayyaki daga ksashen waje batare ta sun taka kafa sun bar Najeriya, ba duk wannan karuwar da fahimta ta dalilin ilimi ne.
Ku biyu mu domin jin cikakkiyar hirar dandali da Malama Nafisa