Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Dauki-Ba-Dadi Da 'Yan Bindiga A Ouagadougou


Hotel Splendid in Ouagadougou
Hotel Splendid in Ouagadougou

Ana can ana dauki-ba-dadi a tsakanin jami'an tsaro da wasu 'yan bindigar da suka kai farmaki kan wasu hoterl hotel a Ouagdougou, babban birnin kasar Burkina Faso.

Wani wakilin sashen Faransanci na VOA ya ce akwai 'yan bindiga su akalla uku da suka kai farmaki kan hotel mai suna Splednid a birnin na Ouagadougou yanzu haka. 'Yan kasashen waje da dama su na zama a wannan hotel din.

A yankin arewacin kasar ma, an kai wani farmaki yau jumma'a a kan wasu jami'an tsaro dake aikin sintiri.

A kasance da VOA domin jin karin bayani.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG