Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe 'Yan BH Tsakanin Najeriya da Chadi


Sojojin Chadi. (File Photo)
Sojojin Chadi. (File Photo)

Gwamnatin kasar Chadi ta ce sojojin ta sun kashe yan Boko Haram akalla 200 da suke fada dasu tsakanin Najeriya da Chadi.

Gwamnatin kasar Chadi ta ce sojojin ta sun kashe yan Boko Haram akalla 200 da suke fada dasu tsakanin Najeriya da Chadi.

Ofishin shugaban kasar Chadi, Idris Deby yace sojojin na Chadi sun fatattaki yan Boko Haram lokacin da suka yi kokarin kawo musu hari, kuma suka kora su zuwa cikin garin Gaborun Ngala dake cikin Najeriya.

Sanarwar tace sojojin Chadin 9 ne suka mutu kana 21 suka samu raunuka sakamakon wannan bata kashin da aka yi tsakanin sojojin da yan boko haram dim, sai dai kawo yanzu ba wani sahihin bayani game da wadanda suka jikkata sakamakon fadan.

Kasar Chadi dai na sahun gaba wajen fada da yan Boko Haram, a kokarin da akeyi na hadin gwiwar makwabtan kasashe wajen taimakawa Najeriya ta kori 'yan Boko Haram,, masu kokarin kafa daular su ta Islama a Najeriya.

A jiya ne Najeriya tace ikon garuruwa kusan sha biyu ya subbuce wa kungiyar ta Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, ciki har da garin Gamborun Ngala.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG