Rahotanni na nuni da cewa, an kashe wani "sojan haya" dan kasar Romania da wasu sojojin Congo biyu, sannan wani sojan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ya jikkata a wasu hare hare uku da suka faru a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a cewar majiyoyi da yawa a jiya Lahadi.
Wani jami'in tsaro a gabashin kasar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an kashe wani sojan haya, wasu uku kuma sun jikkata a ranar Asabar sakamakon wani hari da makami mai linzami da aka kai kan wani sansanin sojan Congo da ke da nisan kilomita 10 daga arewacin birnin Goma.
Ba a dai tabbatar da musabbabin harin ba.
Tsawon watanni kenan dakarun Rwanda da 'yan tawayen M23 suka yi wa babban birnin North Kivu kawanya daga arewa da kuma yamma.
Ana dai gwabza fada a kai-a-kai da sojojin Congo a wajen birnin, yayin da 'yan tawayen da ke samun goyon bayan Kigali ke ci gaba da mamaye gabashin kasar.
Dandalin Mu Tattauna