Gwamnatin Saliyo ta fara jana’izar mutane sama da 350 da suka mutu a wannan mako, bayan da bala’in zaftarewar kasa ya abkawa Freetwon, babban birnin kasar.
Ya zuwa yanzu ba a san inda wasu mutane 600 suke ba, yayin da masu aikin ceto ke ci gaba da kokarin zakulo gawarwakin wadanda bala’in ya rutsa daga cikin tabon kasa da baruguzan gidaje da suka rushe.
A ranar Alhamis din da ta gabata, Shugaba Ernest Bai Koromo ya mika sakon ta’aziyyarsa ga daukacin mutanen kasar, inda ya basu tabbacin cewa gwamnatinsa za ta tallafawa iyalan mamatan da kuma wadanda suka jikkata.
Sai dai gwamnatin kasar ta Saliyo ta sake yin gargadin kan yiwuwar samun wani bala’in zaftarewar kasar, a wani yankin tsauni da ya tsage, inda kuma a ka umurci mazauna yankin da su fice daga wurin.
Kasar ta saliyo dai ta nemi tallafin kasashen duniya yayin da hukumomin lafiya ke kokarin kaucewa barkewar wata cuta.
Facebook Forum