Majalisar Dinkin Duniya ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari akan wani sansanin dakarunta a Timbuktu da ke arewacin Mali, inda suka kashe mutane bakwai.
Jami’an Majalisar Dinkin Duniyan sun ce, daga cikin wadanda suka mutu har da wasu masu gadi ‘yan asalin kasar ta Mali da wani jandarma da kuma wani ma’aikacin kwantiragin kasar dake aiki da ofishin Majalisar Dinkin Duniyar.
Sun kuma ce, dakarunsu su ma sun kashe mahara shida a wannan hari da aka kai da tsakar ranar Litinin.
Harin ya kuma biyo bayan wani makamancinsa da aka kai a jiya Litinin, inda wasu mutane dauke da makamai suka bude wuta akan dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na Mali a garin Douentza da ke tsakiyar kasar.
Wannan hari ya yi sanadin mutuwar sojan wanzar da zaman lafiya na majalisar guda da kuma wani na Mali daya.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres, ya yi Allah wadai da wadannan hare-hare, yana mai cewa, hare-haren, sun fada cikin jerin laifukan yaki a karkashin dokokin kasa da kasa.
Facebook Forum