Kasashen Turai su na kara yawan agajinsu ga dubban ‘yan Iraqi dake neman tserewa daga farmakin mayakan Daular Islama a yankin arewacin Iraqi.
Britaniya da Faransa sun jefo ruwa da abinci da fitilu masu aiki da hasken rana a kan dutsen Sinjar a yau talata, domin taimakawa dubban mabiya addinin yazidi da wasu ‘yan tsiraru da suka gudu kan wannan dutse.
‘Yan gudun hijira kimanin dubu 20 sun samu nasarar tserewa daga kan dutsen Sinjar cikin ‘yan kwanakin nan tare da taimakon sojojin Kurdawa na yankin, amma har yanzu akwai dubbai da suka rage kuma su na karancin ruwa da abinci.
Yayin da wannan matsala ta ‘yan gudun hijira ek wakana kuma, mutumin da aka nada sabon firayim ministan Iraqi jiya litinin, Haider al-Abadi, yana kara samun goyon bayan kafa gwamnati. Amurka ta bayyana goyon bayanta, yayin da kasar Iran makwabciyar Iraqi ta aike da sakon taya shi murna. Wannan da alamun ya kara tauye fatar da firayim minista Nouri al-Maliki ke da shi na ci gaba da rike madafun iko ta hanyar tsawaita shekaru 8 da yayi kan mulki tare da wani sabon wa’adin na uku, na karin shekaru 4.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya roki Abadi da ya gaggauta kafa gwamnati wadda zata wakilci dukkan al’ummar Iraqi, ‘yan Sunni, Shi’a, Kurdawa da sauran ‘yan tsiraru na kasar.