Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Darikar Shiya Sun Yi Gangamin Sallar Ashura A Niger


Gangamin 'yan darikar shiya a Niger
Gangamin 'yan darikar shiya a Niger

Yayinda al’umar musulmi ke shagulgulan sallar Ashura a yau Alhamis ‘yan darikar Shiya a jamhuriyar Niger sun yi gangami domin juyayin rasuwar imam HUSEIN wanda suke zargin cewa makiya ne suka hallakar da shi saboda hassada irin ta Adam.

Mabiya darikar Shiya a karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Lazaret sun yabawa imam HUSSEIN a gangamin da suka shirya domin kara jaddada biyayyarsu a gareshi a wannan rana ta 10 ga watan Muharram, ranar sallar Ashura wace ke matsayin ranar juyayi a garesu.

DAHIROU MOUSA TCHADOUWA na daga cikin mabiya yan darikar Shiya a jamhuriyar Niger. Ya ce rana ce ta juyayi garesu saboda irin kisan da aka yiwa Imam Husein dalilin kiyayyar da ake yiwa iyalan Annabi Muhammad(SWA) a lokacin.

Halin da jagoran ‘yan shiyar Nigeria Sheik Ibrahim Al Zak Zaky ke ciki, biyo bayan arangamar da ta hada magoya bayansa da jami’an tsaro a Zaria na ci gaba da bakanta ran ‘yan shiyan Niger. Dalili kenan da bahasin shugaban mazabahar shiya a Niger Sheik Ahmed Lazaret na ranar ASHURA ya karkata akan wannan al’amari. Ya ce an kona mutane da dama a Zaria an kona gawarwaki saboda suna son gidan Manzon Allah.

Yace kisan da aka yi a Zaria ba zai sa su yi kasa a gwuiwa ba, kuma ba zai sa su zama mahaukata su dauki makami su kashe mutane ba.

Sheikh Ahmed Lazaret ya nuna damuwa akan matsalar tasron dake da nasaba da ayyukan kungiyoyin tayarda kayar baya. Kashe mutum domin bai yi addini ba baya cikin koyaswar addinin musulunci.

Shugabannin darikar shiya a Niger: Daga dama Shaikh Ahmed Lazaret shugabansu
Shugabannin darikar shiya a Niger: Daga dama Shaikh Ahmed Lazaret shugabansu

Mabiya mazabahar shi’ah sun bayyana cewa zasu ci gaba da tarurrukan tunawa da ranar mutuwar imam HUSSEIN har zuwa ranar 20 ga watan Safar yayinda wasu daga cikinsu ke shirye shiryen zuwa Karballah ta kasar Iraq domin ziyarar karrama Imam Husein lokaci guda da takwarorinsu na sassan duniya.

A saurari rahoton Souley Barma

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:01 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG