Gwamnan wanda sakataren gwamnati Taiwo Adeolu ya wakilceshi ya ce sun kira taron ne saboda guje ma irin abubuwan da suke faruwa a jihohi dake makwaptaka da su tsakanin makiyaya da masu gonakai. Ya ce a jiharsu kowa nasu ne sai dai jihar nada dokoki kuma duk wanda ya saba masu za'a hukunta shi koshi wanene. Ya ce gwamnati ba zata tsaya sai lamarin ya faru ba kana a ce za'a yi gyara. Ya ce makasudin kiran taron ke nan.
Abu na biye da shi shi ne domin a fahimci juna shi yasa ana shirya taron daga lokaci zuwa lokaci. Ya shawarci shugabannin su hada hannu da gwamnati domin samun zaman lafiya da cigaban kasa.
Ladan Ibrahim Ayawa nad rahoto.